Hausa Proverbs

1) Karin Magana
A juri zuwa rafi, wata rana za'a faso tulu.

Ma'ana
Idan dai mutum ya cika ganganci tabbas wataran zai gamu da tsautsayi.
2) Karin Magana
A rashin tayi, akan bar arha.

Ma'ana
Rashin gwada yin abu, ya sa ake ganin kamar ba zai yiwu ba.
3) Karin Magana
A saka a baka, ya fi a rataya.

Ma'ana
Duk ƙanƙantar abu matuƙar dai zai yi amfani, yafi ace ba bu shi.
4) Karin Magana
Abokin kuka ba'a ɓoye masa mutuwa.

Ma'ana
Akwai dangantakar da tafi ƙarfin a wulaƙanta ta.
5) Karin Magana
Alamar ƙarfi ta na ga mai kiba.

Ma'ana
Yanayin abu shi zai nuna yadda yake.
6) Karin Magana
Albasa ba ta yi halin ruwa ba.

Ma'ana
Ya na nuna yadda wani ya kauce daga asalinsa.
7) Karin Magana
Allah ya tsari gatari da saran shuka.

Ma'ana
Allah ya haneka da aikata aikin da na sani.
8) Karin Magana
An dade ana ruwa kasa na shanyewa

Ma'ana
An dade ana hakuri da wani abu ko wani mutum.
9) Karin Magana
Ana raba ka da kiwon Kyalla, kana kyalla ta haihu.

Ma'ana
Ana nu na ma illar aikata wani abu, ka na hangen abin da za ka samu a ciki.
10) Karin Magana
Ana zaton wuta a maƙera, sai ta tashi a masaƙa.

Ma'ana
Ana zaton abu a wani wuri sai ya bayyana a inda ba'a tsammaninsa.

MOBILE APP COMING SOON ON